Yan bindiga sun kashe matafiya akan hanyar Katsina-Jibia

Yan bindiga sun kashe wasu matafiya akan hanyar Jibia-Katsina.

Yan bindigar sun kashe mutanen ne a harin da suka kai musu a karamar hukumar Jibia.

Lamarin ya faru ne lokacin da Yan bindigar suka kai farmaki kauyen Farin Bala inda nan take suka kashe direban motar kamfanin sufuri na jihar Katsina wato KSTA.

Maharan sun kuma samu nasarar yin awon gaba da wasu fasinjoji da ba a san yawansu ba.

A wani fefan bidiyo da aka fitar ya nuna yadda ake kwashe wanda suka jikkata da kuma wadanda suka mutu a hari domin kai su Asibiti.

More from this stream

Recomended