
Yan bindiga a ranar Litinin sun yi garkuwa da wani ɗan kasuwa, Nasiru Na’ayya dake kauyen Gangarbi dake karamar hukumar Roggo ta jihar Kano.
Wani shedar gani da ido wanda dan uwa ne ga mutumin ya ce yan bindigar sun farma ƙauyen da misalin ƙarfe 12:00 na dare inda suka fara harbin iska.
“Lokacin da mutanen yankin suka yi yunkurin hana yan bindigar tafiya da mutumin sun harb mutane biyu wanda ya jawo mutuwar mutum guda nan take guda kuma ya jikkata inda yanzu haka yake samun kulawa a asibiti.”
A cewar wani da ya nemi a sakaye sunansa ya ce Gangarbi da makotan ƙauyuka da suka haɗa da Bari da Gwangwan a yan kwanakin nan sun fuskanci hare-hare daga yan bindiga.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce kawo yanzu bashi da masaniya kan harin.