Yan bindiga sun buɗe wuta kan ayarin motocin sanata Ubah

0

Wasu yan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kai harin kwanton ɓauna kan jerin gwanon motocin, Ifeanyi Uba sanata mai wakiltar mazabar Kudancin Anambra.

Lamarin ya faru ne a kauyen Enugwu-Ukwu dake karamar hukumar Njikoka ta jihar.

Wasu majiyoyi da suka sheda faruwar lamarin sun bayyana cewa mutane shida aka kashe a harin ciki har da yan sanda da kuma masu taimakawa sanatan.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar,Ikechukwu Ikenga ya tabbatar da faruwar lamarin sai da ya ce ba shi da masaniyar mutane nawa ne suka mutu a harin.

Jihar Anambra ta dade tana fama da hare-haren yan bindiga da ake zargin mayakan kungiyar IPOB da kaiwa.