Wata gobara ga ƙone wata mata da ƴaƴanta uku ƙurmus a Kano

Al’ummar Agadasawa a jihar Kano sun shiga cikin mummunan yanayi bayan da wata gobara ta tashi tare da halaka wata mata da ‘ya’yanta uku.

Mummunan lamarin da ya jawo juyayin dubban jama’a a fadin jihar.

An ce lamarin ya faru ne da tsakar daren ranar Laraba a lokacin da marigayan ke barci.

Marigayiyar, Zainab, da ‘ya’yanta uku, Amatullahi, Amaturrahman, Safiyya, da Muhammad, iyalan wani dan kasuwan Kano ne mai suna Ado Muhammad Uba.

Wani dan uwansa mai suna Jazuli Jibril Aminu ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a lokacin da aka dawo da wutar lantarki, inda matar ta manta da kashe firjin da ta saka, wanda hakan ya yi sanadiyar fashewar silindar gas din.

A cewar Aminu, Zainab cikin takaici ta yi kokarin ceto ‘ya’yanta daga gobarar, amma kokarinta ya ci tura.

More from this stream

Recomended