‘Yar kasar Bulgariya Liliana Mohammed ‘yar shekaru 62 da haihuwa ta yi nasarar haddar Alkur’ani mai girma a jihar Kano, wanda ya zama wani gagarumin ci gaba a tafiyarta a Musulunci.
Rahotanni sun ruwaito alakar Liliana da Kano cewa ta faro ne shekaru 32 da suka gabata, lokacin da aure ya kai ta jihar tana da shekaru 30.
Marigayi mijinta, Alhaji Ibrahim Sambo, dan kasuwa ne da ake girmamawa a yankin.
Da take magana da manema labarai, Liliana ta bayyana cewa hanyarta ta zuwa addinin Musulunci ta faro shekaru goma da suka wuce ne lokacin da ta rungumi addinin kuma ta fara koyon karatun kur’ani.
Duk da shekarunta, Liliana ta yi karatu a gida, karkashin jagorancin malamarta, Malama Hafsa.
Wata Baturiya ‘yar Bulgaria Liliana Mohammed ta haddace Alkur’ani mai girma a Kano
