Wani Matashi Ya Mutu A Cikin Ruwa A Kano

Wani matashi dan shekara 20 mai suna Salisu Tasiu Muhammad ya nutse a kududdufin Bakin Gada dake garin Bunkure a karamar hukumar Bunkure ta jihar Kano.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis inda ya ce an fito da Tasiu baya cikin hayyacinsa amma daga bisani likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Abdullahi ya kara da cewa tuni aka mika gawarsa ga mahaifinsa, Alhaji Tasiu Muhammad.

More from this stream

Recomended