Wani Matashi Ya Kashe Mahaifiyarsa Bayan Da Taki Bashi ₦10,000

Rundunar yan sandan jihar Rivers, ta kama wani matashi mai suna Osaro Owate kan zargin kisan mahaifiyarsa a unguwar Elesa dake karamar hukumar Eleme ta jihar.

Matashin ya aikata kisan kan ne bayan da sabani ya shiga tsakaninsu kan naira 10,000

Wanda ake zargin dai yayi ikirarin cewa yana fama da cutar aljanu sama da shekaru 30 ya amince da yin amfani da fatanya wajen kisan mahaifiyar.

Da yake magana cikin wani fefen bidiyo da aka naɗa Owate ya ce ya faɗa mahaifiyarsa taje banki ta ciro kuɗi domin ta bashi ₦20,000 ya sayi kayan da zai saka a wajen wani bikin mutuwa amma a maimakon haka sai kawai ta bashi 10,000 abin da ya jawo cacar baki har ta kai ga ya kashe ta.

More from this stream

Recomended

Trump Ya Yaba Wa Tinubu Kan Yaƙi Da Ta’addanci A Najeriya

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yaba wa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, kan abin da ya bayyana a matsayin ƙwazon jagorancinsa wajen yaƙi da ta’addanci da magance matsalar tsaro a ƙasar. A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, Trump ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa Tinubu. Ya ce yana yaba wa shugaban […]