Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Uba Sani ya yi kira da jami’an sojoji da su cigaba da zafafa kai farmaki kan yan fashin daji dake faɗin jihar.
Gwamnan ya yi wannan rokon ne biyo bayan hare-haren da aka kai ƙananan hukumomin Igabi da Kauru inda aka kashe mutane shida tare da yin garkuwa da wasu biyar.
Rahotannin sun bayyana cewa an kai harin ne da misalin ƙarfe 10 na daren ranar Juma’a.
Kwamishinan ma’aikatar cikin gida da kuma tsaro, Samuel Aruwan shi ne ya bayyana haka a madadin gwamnan lokacin da suka kai ziyarar gani da ido kan yadda yanayin tsaro yake a ƙauyukan Gwada da Karawa a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar.
A yayin ziyarar Aruwan na tare da manyan sojoji da sauran shugabannin hukumomin tsaro.
“Mun zo nan a madadin gwamnan Uba Sani domin muyi muku ta’aziyar rayukan da aka rasa a mazabun Kerawa da Sabon Birni a ƙaramar hukumar Igabi da kuma Kwassam, Kurera da Kan Makama a ƙaramar hakumar Kauru,” a cewar Aruwan.
Tawagar ta gana da shugabannin al’umma a yankin ƙarƙashin jagorancin mai rikon muƙamin hakimin Sabon Birni, Ahmed Aliyu.