Tsohon gwamna Shema ya ziyarci gwamna Dikko Radda

Tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema ya ziyarci gwamna mai ci, Dikko Radda a gidan gwamnatin jihar.

Shema wanda ya mulki jihar Katsina daga shekarar 2007 zuwa 2015 a karkashin jam’iyar PDP ya kai ziyarar ne tare da yan tawagarsa.

A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga gwammnan jihar kan kafafen sadarwar zamani, Isah Miqdad ya fitar ya ce tsohon gwamnan ya ce ya kai ziyarar ne domin taya gwamna Radda murna kan yadda aka rantsar da shi lafiya.

Shema ya ce jihar Katsina na bukatar mutane irin Radda domin kawo cigaba ya kuma yaba da kokarinsa na dawo da jihar turbar cigaba kamar yadda take a baya.

A nasa jawabin gwamna Radda ya godewa tsohon gwamnan kan ziyarar da kuma yi masa murna kan gudunmawar da ya bayar wajen samun nasarar yin zaben da aka yi lafiya.

More from this stream

Recomended