Tinubu ya karɓi Anyim Pius a jam’iyar APC

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya yi wa  tsohon shugaban majalisar dattawa,Anyim Pius Anyim maraba da zuwa  jam’iyar APC.

A makon daya gabata ne Anyim ya sanar da shigarsa jam’iyar APC a mazaɓarsa dake jihar Ebonyi.

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma  da Francis Nwifiru na jihar Ebonyi su ne suka jagoranci shugaban majalisar dattawan ya zuwa fadar Aso Rock a ranar Laraba.

Da yake magana da manema labarai bayan ganawa da shugaban ƙasar, Anyim ya ce gwamnatin shugaban ƙasa Tinubu na yin yadda yakamata wajen kulawa da buƙatun ƴan Najeriya.

Ya ce akwai buƙatar ƴan Najeriya su dunƙule waje ɗaya su tabbatar cewa ƙasar ta cigaba.

Sauya sheƙar da Anyim ya yi ta kawo ƙarshen tsawon shekaru 24 da ya shafe a cikin jam’iyar PDP inda ya riƙe muƙamin shugaban majalisar dattawa da kuma sakataren gwamnatin tarayya.

More from this stream

Recomended