Tinubu ya gana da Sarki Charles

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga Sarki Charles na Birtaniya a fadar Buckingham a wata ziyara da yakai.

Wannan ce ganawa ta farko da shugabannin biyu suka yi tun bayar wacce suka yi a birnin Dubai a wurin taro kan sauyin yanayi na COP 28 da aka yi a shekarar da ta wuce.

A cewar mai magana da yawun shugaban ƙasa , Bayo Onanuga Sarki Charles ne ya buƙaci ganawar.

Onanuga ya ce dukkanin shugabannin biyu sun tattauna kan abubuwan da suka yi tarayya akai ciki har da batun gaggauta mayar da hankali kan  sarkakiyar dake tattare da batun sauyin yanayi.

Tinubu da Sarki Charles  sun duba batun lalubo damarmaki dake buÆ™atar haÉ—a karfi da Æ™arfe dan tunkarar taron COP 29 da za ayi a Æ™asar  Azerbaijan da kuma taron kasashe rainon Ingila da za ayi a Samoa.

More News

Gwamnatin Enugu ta bayyana dalilin sanya haraji kan gawar mutane

Gwamnatin Jihar Enugu a ranar Lahadi tayi ƙarin haske kan matakin da ta ɗauka kan sanya haraji akan gawar mutane dake ajiye a ɗakin...

ÆŠan tsohon gwamnan Kaduna Ahmad Makarfi ya rasu a hatsarin mota

Faisal Makarfi dan gidan tsohon gwamnan jihar Kaduna Ahmad Muhammad Makarfi ya rasu. Faisal ya rasu a wani hatsarin mota da ya faru akan hanyar...

Ƴan sanda sun kama mutane 6 da ake zargi da kisan kai da fashi da makami a Gombe

Rundunar ƴan sandan jihar Gombe ta ce a cikin mako guda  jami'an ta sun kama wasu mutane 6 da ake zargi da aikata fashi...

Ƴan sanda sun kama wani fursuna da ya tsere daga gidan Gyaran Hali na Maiduguri

Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta ce jami'an ta sun kama Kyari Kur ɗaya daga cikin ɗaurarrun da suka tsere daga gidan gyaran hali ...