Sojojin Najeriya sun kama waɗanda ake zargi da garkuwa da wani janar

Sojojin Najeriya sun kama wasu mutane hudu da ake zargi da yin garkuwa da Manjo Janar Richard Duru mai ritaya tare da kin karbar cin hancin Naira miliyan 5 duk da cewa sun kwato tarin makamai da alburusai daga hannun wadanda ake zargin a jihar Imo.

Hakazalika sojojin sun kuma kashe ‘yan ta’adda bakwai a jihohin Borno da Yobe yayin da wasu goma sha daya (11) suka mika wuya ga jami’an sojin na Najeriya.

Wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar a ranar Laraba kan shafinta na X ta bayyana cewa, sojojin a jihar Imo, sun yi nasarar bibiyar wasu mutane hudu da ake zargi da hannu a kisan Janar din sojan mai ritaya.

Sanarwar ta kara da cewa wadanda ake zargin, “lokacin da aka kama su, sun yi yunkurin baiwa sojojin cin hancin Naira miliyan biyar (N5,000,000), amma sojojin sun ki amincewa da hakan.

A maimakon haka, sojojin sun kwace kudaden cin hancin da suka kai N5,048,105, tare da motoci uku, kwamfutoci shida da na’urar tantance kudi.

A bangare guda kuma, a ranar 27 ga watan Agusta, 2024, sojojin da ke aiki da sahihan bayanan sirri, sun yi wa ‘yan ta’addan Boko Haram kwanton bauna a kauyen Logomani da ke karamar hukumar Ngala a jihar Borno.

More from this stream

Recomended