Sojoji sun kashe mayaƙan ISWAP 5 tare da lalata sansaninsu 4 a Borno

Sojojin rundunar kasa da kasa dake samar da tsaro a yankin tafkin Chadi sun kashe mayaƙa 6 na ƙungiyar ƴan ta’adda ta ISWAP a jihar Borno.

Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi shi ne ya bayyana haka inda ya ce an kai farmakin ne kan ƴan ta’addar da haɗin gwiwar rundunar samar da tsaro ta Operation Hadin Kai.

Zagazola ya bayyana cewa sojoji sun kaddamar da farmaki kan maboyar yan ta’addar a ranar 4 ga watan Disamba.

Wata majiyar jami’an sojan leƙen asiri ta bayyana cewa sojojin sun tarwatsa sansanonin ƴan ta’addar guda huɗu dake kauyukan Ngurnoa, Gumnari, Naira da Amburam a ƙaramar hukumar Monguno ta jihar Borno.

Majiyar ta ce sojoji sun yi musayar wuta da ƴan ta’addar abun da ya tilasta musu tserewa ta cikin ruwa har ta kai ga an kashe biyar daga cikin su.

Ɗaya daga cikin jami’an sojojin da suka kai farmaki ya samu rauni kuma tuni aka ɗauko a jirgin sama ya zuwa asibitin sojoji dake Maiduguri.

Sojojin sun gano bindiga kirar GPMG gidan saka harsashi na bindigar AK-47 guda a cikin wani bangare na ruwan da bashi da zurfi

More from this stream

Recomended