Sojan Ruwan Najeriya Sun Kama Wasu Mutane Uku Da Suka Ɓuya A Cikin Farfelar Jirgin Ruwan Da Zai Tafi Nahiyar Turai

Dakarun rundunar sojan ruwan Najeriya dake aiki da jirgin NNS Beecroft sun kama wasu mutane uku da suka shiga cikin farfelan wani jirgin ruwan mai dake kan hanyar sa ta zuwa nahiyar Turai.

Kolawole Oguntuga, kwamandan jirgin NNS Beecroft ya ce mutanen da suka boye a cikin jirgin an kama su ne a ranar Laraba a yayin sintiri biyo bayan bayanan sirri da rundunar ta samu daga imda jirage suke tsayawa a cikin tekun Lagos

Ya ce mutanen uku sun boye ne a cikin inda farfelan jirgin take bayan da wasu masunta suka karbi N20, 000 daga mutane biyu daga ciki a yayin da mutum guda ya biya 5000 kana suka saka su a jirgin.

Mutane uku sun haɗa da Ebuka Daniel mia shekaru 29 daga Enugu, Samuel Abraham mai shekaru 32 daga jihar Edo sai kuma Christian Happy daga jihar Delta.

More from this stream

Recomended