Siyasa da addini ne ‘suka hana shawo kan rikici a Kudancin Kaduna’ | BBC Hausa

El Rufai

A jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya masu ruwa da tsaki na ci gaba da nuna damuwa kan rikice-rikice masu nasaba da kabilanci da addini da suka addabi yankin kudancin jihar.

Tsohon mataimakin gwamnan jahar Barnabas Bala Bantex ya shaida wa BBC cewa ana amfani da siyasa wurin raba kan al’umma, wanda ke ci gaba da rura wutar rikicin addini da na ƙabilanci.

Ya ce ba shakka akwai mutanen da ke amfani da rikicin don samun riba a siyasar su.

Tsohon mataimakin gwamnan ya ce yana takaicin baza sojoji a kudancin jahar, wanda a cewar sa hakan zai hana ‘yan kasuwa shigowa jahar don zuba jari.

A kan haka yake ganin dole ne masu ruwa da tsaki a cikin al’umma su hadu wuri ɗaya don samar da mafita.

Kaduna na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya mafi fama da matsalolin tsaro kama daga hare-haren ‘yan fashin daji a yankin Birnin Gwari da kuma rikicin ƙabilanci musamman a yankin Kudanci.

Kimanin shekara 40 ke nan ake ta fama da wannan rikici na Kudancin Kaduna, kuma lamarin na so ya gagara.

Ko a baya-bayan nan, rahotanni sun ce an kashe gomman mutane a rikicin ta hanyar kai hare-hare masu kama da na sari-ka-noƙe a yankin.

More from this stream

Recomended