Sashen Hausa Na Muryar Amurka Ya Gudanar Da Taron Hadin Kai A Abuja | VOA Hausa

Taron tattaunawar dai ya samu halartar wakilan mazhabar Shi’a da Izala da kumaTijjaniya, sai kuma rundunar yan sanda da Lauyoyi da jami’an tsaro, masu kare hakkin mata da jami’an gwamnati da kuma Pasto Aminci a bangaren addinin Kirista.

Haka kuma taron ya duba muhimmancin bin dokokin kasa da kaucewa fito-na-fito da jami’an tsaro tare da bin ka’idar fitowa zanga-zanga ga kungiyoyin dake da irin wannan tsari.

Dr. Umar Labdo shine ya wakilci kungiyar Izalatul Bidi’a wa Iqamatus-Sunnah (JIBWIS), ya yin da Muhammad Ibrahim Gamawa ke wakiltar Mazhabar Shi’a, Muhammad Alkasim Yahya a matsayin wakilin Ansaruldin Attijjaniya, inda suka baiyyana jin dadinsu game da taron, da kuma jaddada muhimmancin zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Pasto Aminci Abu da tsohon shugaban reshen matasa na kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Pasto Simon A.S Dolly, sun halarci taron a madadin mabiya addinin Kirista.

Irin waddan taruka kan taimaka wajen fahimtar juna da zai iya zama yunkuri kan wanzar da zaman lafiya a kasa.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...