NDLEA ta kama hodar iblis da tramadol da aka boye a cikin takalmi

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta yi nasarar kama wasu muggan kwayoyi guda biyu, inda ta gano hodar iblis da aka boye a cikin safofin takalma da kwayoyin tramadol da aka boye a cikin kwantena.
 
Daraktan yada labarai na hukumar Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya gargadi matafiya da su yi taka-tsan-tsan wajen karbar kaya ko kayayyaki daga hannun wasu don tafiya musu da shi.
 
A cewar Babafemi, an gano hodar iblis ɗin ne a cikin tafin takalmin da aka nufi Turai, yayin da aka gano kwayoyin tramadol a boye a cikin kwantena.

More from this stream

Recomended