Nan ba da jimawa ba za mu kamo Bello Turji

Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya sha alwashin ganin an cafke fitaccen madugun ‘yan ta’adda, Bello Turji, nan ba da jimawa ba.

Janar Musa ya ba da wannan tabbacin ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida kan ayyukan da sojoji ke yi a fadin kasar a ranar Talata a Abuja.

Babban hafsan tsaron ya jaddada cewa sojojin na bin dan ta’addan ne, inda ya kara da cewa suna gab da kama shi duk da cewa yana iya daukar lokaci.

Dangane da zargin sanya harajin da aka yi wa al’ummomi da dan ta’addan ya yi, Janar Musa ya ce sojoji suna aiki tare da sauran jami’an tsaro da gwamnatin jihar domin samar da isasshiyar kariya ga mutanen wajen.

More from this stream

Recomended