Mutane 74 sun kamu da cutar zazzaÉ“in Lassa cikin mako guda – NCDC

Hukumar NCDC dake yaki da cututtuka masu yaɗuwa ta tabbatar da cewa mutane 74 ne suka kamu da cutar zazzaɓin Lassa a makon da ya wuce.

A jihohi 9 ne aka samu karin mutanen da suka kamu da cutar mai haÉ—arin gaske inda jihar Ondo take kan gaba da yawan mutane.

Mutane 28 ne suka kamu da cutar a jihar Ondo sai jihar Bauchi da Edo dake da mutane 18 kowaccen su.

Sauran jihohin da aka samu bullar cutar sun hada da Oyo (3), Ebonyi(3), Benue(1),Katsina(1),Taraba(1) da kuma Kaduna(1).

Cutar zazzaɓin Lassa na hatsari sosai inda take da saurin kisan waɗanda suka kamu da ita.

More News

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...