Ministoci:Buhari ya tura sunayen mutane 7 ga Majalisar Dattawa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tura saunayen mutum bakwai zuwa Majalisar Dattawa a matsayin wanda za a nada sabbin ministoci.

Sunayen mutanen na ƙunshe ne cikin wata wasika da fadar shugaban kasar ta tura ga majalisar dauke da sunayen mutanen wadanda za a tantance su kafin tabbatar musu da mukaman.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 wa’adin mulkin Buhari zai kare.

Sunayen mutanen da Buhari ya tura majalisar sun hada da Henry Ikechukwu Iko (Abia) Umar Ibrahim El-Yakub (Kano) da kuma Joseph Ukama (Ebonyi.)

Sauran sun hada da Umana Okon Umana (Akwa Ibom) Adewole Adegoroye (Ondo) Odum Udi (Rivers) da Goodluck Nnana Opia (Imo.)Anan gaba kadan ne majalisar za ta saka rana domin tantance mutanen.

More News

Mayakan Boko Haram 314 sun mika wuya ga sojoji a Bama

Rundunar sojan Najeriya na cigaba da samun gagarumar nasara a yakin da take da mayakan Boko Haram.. A sakamakon kakkauta farmaki da hare-hare da rundunar...

Mayakan Boko Haram 314 sun mika wuya ga sojoji a Bama

Rundunar sojan Najeriya na cigaba da samun gagarumar nasara a yakin da take da mayakan Boko Haram.. A sakamakon kakkauta farmaki da hare-hare da rundunar...

Nigeria suffering from bad leadership, crisis looming, says Peter Obi

Labour Party (LP) presidential candidate, Peter Obi has stated that Nigeria is suffering from bad leadership, and there might be a crisis in the...

Workers’ Strike: Gov. Abiodun meets Labour leaders

Ogun State Governor, Prince Dapo Abiodun, has invited Organised Labour in the State to a meeting, today, Wednesday to resolve the industrial action embarked...