Messi Ya Fi Kowa Zura Kwallaye a Turai

Hakkin mallakar hoto: Getty images

Dan wasan Argentina da Barcelona, Lionel Messi, shi ne wanda ya fi kowa zura kwallaye a gasar lik-lik ta nahiyar Turai a bana.

Dan wasan, wanda shi ne kyaftin din Barcelona, ya ci kwallaye guda 16 a La Ligar bana, har da wadda ya zura a ragar Getafe a ranar Lahadi da kungiyar Nou Camp ta yi nasara da ci 2-1.

Messi ya ci kwallo 16 a wasa 18 da ya yi a La ligar 2018/19, kuma kungiyoyi 10 ya zura wa kwallayen a raga.

Kyaftin din Argentina ya ci Getafe a farkon Janairun 2019, ya taba yin irin wannan bajintar a 2017 da ya zura kwallo a ragar Villareal da kuma Levante a 2018.

Messi yana da maki 32, da yake duk kwallo daya maki biyu keda ita, wanda yake mataki na biyu shi ne Liu mai taka leda a Kalju ta Estonia.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...