Connect with us

Hausa

Me ya sa sojoji ke ci gaba da karbe iko a nahiyar Afirka?

Soldiers in Sudan

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Sojoji sun yi wa Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir juyin mulki, sakamakon zanga-zangar nuna adawa da mulkinsa da ta mamaye titunan kasar.

Rundunar sojan kasar ta yi alkawarin gudanar da harkokin mulkin na tsawon shekara biyu, inda daga bisani za ta gudanar da zabe.

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya kama ragamar mulkin kasar ne bayan wani juyin mulkin da aka yi cikin shekarar 1989, kodayake kafin juyin mulkin an sha yin yunkuri da dama, wasu sun yi nasara, wasu kuwa hakarsu ba ta cimma ruwa ba.

An gudanar da cikakken bincike ne kan tarihin juyin mulkin soja a kasar Sudan, tare da nau’ukansa a daukacin fadin Afirka

Sudan ta yi fama da yawan yunkurin juyin mulki fiye da kowace kasa a Afirka

Daukacin juyin mulkin da ya hada da na baya-bayan nan, an yi a kalla yunkuri sau 15 – hudu ne kawai suka samu nasara.

Yanzu haka dai rundunar soja ta samu nasarar hambarar da Omar al-Bashir, za a iya cewa wannan shi ne karo na biyar.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jama’a sun yi murna a fili bayan da sojoji suka taimaka wajen sauke Mugabe a 2017

Mene ne juyin mulki?

Tun cikin shekarun 1950, an yi yunkurin juyin mulkin da yawansu ya kai 206 a fadin Afirka, kamar yadda wasu masanan kimiyyar siyasa ‘yan Amurka biyu suka tattara bayanai akai, wato masanan su ne, Jonathan Powell and Clayton Thyne.

Ma’anar juyin mulki shi ne wani yunkuri da ya sabawa doka da sojoji ko kuma jami’an farar hula ke yi domin hambarar da gwamnati mai ci.

Sai dai ma’anar juyin mulki an sha yin takaddama a kanta, ta yadda a da can, shugabannin soja suka musanta cewa suna aiwatar da lamarin.

Alal misali, kasar Zimbabwe a shekarar 2017 sojojin kasar sun yi juyin mulkin da ya kawo karshen mulkin Robert Mugabe na shekaru 37. A lokacin, wani babban jami’in soja Manjo-Janar Sibusiso Moyo, ya shiga talabijin, inda ya karyata juyin mulkin sojan.

“Shugabannin juyin mulki kusan koda yaushe sukan karyata aiwatar da juyin mulkin a kashin kansu a kokarinsu na ganin cewa sun samu amincewar doka, “in ji Powell.

Powell da Thyne sun yi nuni da cewa juyin mulkin da ya samu nasara, shi ne, wanda ya kama ragamar mulki tsawon lokacin da ya zarta kwanaki bakwai.

In an cire dayan nan, wanda aka gudanar a Sudan, an yi yunkurin juyin mulki har sau 105, wadanda ba su samu nasara ba a fadin Afirka da kuma guda 100 da suka kai ga gacin nasara.

Kasar Burkina Faso da ke Afirka ta Yamma ita ke da yawan juyin mulkin da suka kai ga nasara, inda adadinsu ya kai bakwai.

Shin Afirka na da karancin juyin mulkin soja?

Tabbas Afirka ta yi fama da dimbin juyin mulkin soja, amma hakika irin wannan tursasawar ta kawo sauyi na matukar raguwa.

Cikin shekaru arba’in, wato tsakanin shekarun 1960 zuwa 2000, yawan yunkurin juyin mulki yana nan daram kan turbarsa na akalla 40 cikin shekaru goma.

Tun daga wancan lokacin an yi matukar samun raguwar lamarin.

A shekarun 2000 an yi yunkurin juyin mulki da yawansu ya kai 22, kuma a daidai ma’aunin shekaru goman da ake kai yawan juyin mulki ya tsaya ne akan 17.

“Kasashen Afirka sun yi fama da yanayin da ke bayar da kafar yin juyin mulki, al’amuran da suka hada da talauci da matsalar tattalin arziki. Da zarar kasa ta yi fama da juyin mulki sau daya, to tamkar ya zama manuniya ce da ke bayar da tabbacin aukuwar wasu da dama.”

Tarihi ya nuna cewa a kasashen Afirka, rundunar soja na taka muhimmiyar rawa wajen mika mulki, tare da tunkarar matsalolin cikin gida da harkokin tsaro.

A fadin duniya

Yawan yunkurin juyin mulkin da aka yi a daukacin fadin duniya, tun daga shekarar 1952 yawansa ya kai 476

Afirka ta yi fama da juyin mulki fiye da kowace nahiya.

Mai biye mata ita ce nahiyar Kudancin Amurka, wadda aka yi mata yunkurin juyin mulki 95, kuma 40 daga cikinsu sun kai ga nasara.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Zanga-zanga a Venezuela a wani yunkuri na hambarar da gwamnatin marigayi Shugaba Chavez

Cikin shekaru ashirin da suka gabata an samu raguwar yawan juyin mulki a nahiyar Kudancin Amurka. Na karshensu dai shi ne wanda aka yi a kasar Venezuela cikin shekarar 2002, don kawar da Shugaba Hugo Chavez, amma bai samu nasara ba.

Powell ya ce kawo karshen yakin cacar baki, al’amarin da ya bayar da kafa ga Amurka da Tarayyar Sobiyat suka rika yin katsalandan a harkokin nahiyar Amurka ta Latin (Ko Kudancin), tare da aniyar hukumomin duniya na kakaba takunkumi ga kasashen da suka yi juyin mulki, kamar Haiti a shekarar 1994, shi ya haifar da raguwar juyin mulkin soja.

Facebook Comments
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Masu zanga-zanga sun yi galaba kan soja a Sudan

Zanga-zangar Sudan

Wasu jiga-jigan gwamnatin mulkin soja su uku a Sudan sun mika tayin sauka daga kan mukamansu- wata muhimmiyar bukata ce ta masu zanga-zanga a kasar.

Ana kallon manyan janar-janar din a matsayin manyan na-hannun daman tsohon shugaba Omar al-Bashir.

Matakin ya zo ne bayan tattaunawa tsakanin sojoji da jam’iyyun adawa kan yadda za a kafa gwamnatin farar hula.

A wani taron manema labarai, kakakin rundunar sojan kasar Laftanar Janar Shamseddine Kabbashi ya ce bangarorin biyu sun cimma matsaya kan mafi yawan bukatun kuma sun yanke shawarar kafa kwamitin hadin gwiwa don warware duk wasu matsaloli.

Jagororin zanga-zanga a Sudan din sun kira wani maci na mutum miliyan daya a yau Alhamis domin matsawa majalisar koli ta sojan kasar mika mulki ga gwamnatin farar hulla.

Jiragen kasa makare da mutane na isa Khartoum, babban birnin kasar don shiga gangamin da za a yi a wajen shelkwatar rundunar soji.

A karon farko, alkalai sun bayyana cewa za su shiga zanga-zangar don nuna goyon bayansu, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

An yi jana’izar mutum 19 a Jigawa

FRSC

An yi jana’izar mutum 19 da suka mutu sanadiyyar wani hadarin mota a karamar hukumar Gwaram da ke jihar Jigawa ranar Laraba.

Hadarin ya faru ne a garin Gwaram Sabuwa da misalin karfe 11:30 na dare, bayan da tayar gaban motar da ke dauke da fasinjoji 40 ta fashe.

Rahotanni sun ce daga nan ne sai motar ta wuntsula kafin ta kama da wuta. Mutum 21 daga cikin fasinjojin ne dai suka ji rauni.

Wani da abin ya faru a kan idonsa ya ce gawarwakin fasinjojin sun kone “kurumus ta yadda ba za a iya gane su ba.”

“Na ga gawarwakin jarirai shida tare da gawarwakin iyayensu,” in ji shi.

Mutanen da hadarin ya rutsa da su wadanda galibinsu mata ne da kananan yara suna kan hanyarsu ta dawowa daga daurin aure ne.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Zaman fursuna na shekara 3 ko tarar $3,000 ga masu shan shisha

shisha

Wuraren da ake shan tabar shisha a Ghana za su dinga fuskantar hukunci mai tsanani idan har ba su bi dokokin kiyaye lafiya da kasar ta tanadar ba.

Shan tabar Shisha dai ya zama ruwan dare a tsakanin matasa a kasar.

Sai dai akwai sabanin ra’ayi kan cewa tabar shisha ba ta da illa kamar taba sigari.

Amma Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO da Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Ghana FDA, ba su yarda da wannan batu ba.

Hukumar ta ce daga yanzu duk mai mashayar da aka kama ana shan shisha a wajen zai fuskanci zaman gidan yari na shekara uku ko a ci shi tarar dala dubu uku, kwatankwacin naira miliyan daya da 80,000 kenan.

Sai dai wannan hukunci zai hau kansu ne kawai idan ba su yi rijistar shishar ba ko kuma idan ba su sanya sanarwar gargadi kan irin hadarin da ke tattare da shanta yake ba.

Yayin shan shisha

Shan wannan taba mai kanshin gaske na kara karbuwa a wurin jama’a a fadin duniya, amma masana harkar lafiya sun ce mafi yawan wadanda suke shanta ba su san hadarin da ke tattare da hakan ba.

Yanzu dai mutane ne da dama suke cin moriyar wannan taba wadda ke tashe a Indiya da Gabas ta tsakiya inda aka ce daga nan ta samo asali.

A Gabas ta tsakiya yayin ya ratsa har tsakanin ‘yan yara maza da mata da ma manyan mata wadanda yawancinsu ba sa shan taba.

Wannan yayi yanzu ya kai har ga kasashen Turai da Brazil da kuma Amurka inda za ka ga shagunan shan wannan taba mai zamani.

Shugaban sashen tiyatar zuciya a babban asibitin kasa na Saudi Arabia, National Guard Health Affairs, Farfesa Hani Najm, ya taba sheda wa BBC a wata tattaunawa cewa yana fargaba shan tabar shisha zai iya kara yawan masu cutukan zuciya a kasashen yankin Gabas ta tsakiya.
Facebook Comments
Continue Reading
Advertisement
Advertisement

Trending

%d bloggers like this: