Har yanzu babu labarin matan da aka sace a wannan makon a Zamfara

Wasu ‘yan bindiga a wannan makon sun sace zawarawa da ‘yan mata da ƙananan yara, wadanda yawansu ya kai 23.

An sace su ne a yankin Ƙaramar Hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

A ranar Laraba ne lamarin ya faru, amma nisa da rashin samun yadda bayanai za su fita ya sa ba a ji labarin sace matan ba sai a jiya Alhamis.

Mazauna yankin Muradun na kukan cewa ayyukan ‘yan fashin daji da ake ta yaɗa cewa sun ragu “ba haka abin yake ba” kawai dai ji ne ba a yi, in ji wani rahoton BBC Hausa.

BBC ta ambato wani magidanci yama cewa, “matan sun fita bayan gari ne yin itace suka ci karo da ‘yan bindigar.

“Duk safiya suna tafiya daji yin itace, a wannan karon tawaga ce ta zawarawa da ‘yan mata da matan da mazajensu suka mutu da kuma ƙananan yara abin ya rutsa da su.

“Da wannan itacen da suke yi, da shi suke samu su ci abinci,”

More from this stream

Recomended