Majalisar wakilai na son a  hana sayar da giya da ƙwaya a tashoshin mota

Majalisar wakilai ta tarayya ta yi kira ga gwamnatin tarayya, jihohi da kuma na ƙananan hukumomi da su hana sayar da giya, ƙwayoyi da kuma sauran abubuwan da suke saka maye a tashoshin mota dake faɗin ƙasarnan.

Har ila yau majalisar ta kuma yi kira ga hukumar NDLEA dake yaƙi da hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi da ta baza komarta a tashoshin mota dake faɗin Najeriya domin kamawa tare da hukunta diloli da kuma masu shan miyagun ƙwayoyi.

Majalisar ta  amince da haka ne biyo bayan ƙudirin da wakili a majalisar ,Abbas Adigun ya gabatar a yayin zaman majalisar na ranar Alhamis.

Da yake gabatar da kuɗirin, Adigun ya koka cewa tashoshin mota sun zama cibiyar sayar da giya da miyagun ƙwayoyi inda direbobi suke sha kafin su hau kan kwalta su na  jefa rayuwar fasinjoji cikin hatsari.

Ya ce hukumar kiyaye afkuwar hatsura ta ƙasa FRSC ta fitar da wani rahoto dake cewa kaso 90 na hatsarin da ake samu a titunan ƙasarnan shan giya da kuma miyagun ƙwayoyi ne yake haddasa su.

Bayan amincewa da kuɗirin da majalisar tayi ta kuma shawarci hukumar ta FRSC da ta riƙa zuwa tashar motoci domin gwada direbobi domin tabbatar da cewa basa cikin maye kafin su hau kan kwalta.

More from this stream

Recomended