Kotun ɗaukaka ƙara ta  tabbatar da zaɓen gwamnan jihar Kogi

Kotu ɗaukaka ƙara dake Abuja ta tabbatar da nasarar Usman Ododo a matsayin halastaccen zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kogi.

A hukuncin da kotun ta zartar ranar Alhamis  rukunin alƙalan kotun su uku sun yi watsi da ƙarar da ɗantakarar jam’iyar SDP Murtala Ajak ya shigar gabanta.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC ta sanar da Ododo ɗantakarar jam’iyar APC a  matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kogi da aka gudanar ranar 11 ga watan Nuwambar 2023.

Ododo ya lashe zaɓen da kuri’a 446,237 inda ya kayar da Ajaka wanda ya samu kuri’a 259,052 a yayin da sanata Dino Melaye na jam’iyar PDP ya samu kuri’a 46,362.

A hukuncin da kotun ta yanke ta ce hujjar da masu ƙara suke da ita kan batun yin jabun takardu da kuma batun rashin cancantar tsayawa takara shari’a ce da ya kamata ayi ta kafin zaɓe.

Kotun ta kuma soki masu ƙara kan yadda suka gaza gabatar da ƙwararan shedu da za su tabbatar da zargin da suke.

More from this stream

Recomended