Kotu ya yanke wa wani sojan bogi hukuncin ɗaurin wata 6

A ranar Alhamis ne wata kotu mai daraja ta daya da ke Dei-Dei, Abuja ta yanke wa wani mutum mai suna Lawal Babangida mai shekaru 31 hukuncin daurin watanni shida a gidan yari bisa samunsa da laifin bayyana kansa a matsayin jami’in soja.

Kotun dai ta tuhumi Babangida, wanda ke zaune a kauyen Tungamaji Abuja da laifin aikata laifuka, cin zarafi, da kuma karbar kudi.

Sai dai mai laifin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, sannan ya roki kotun da ta yi masa sassauci.

“Don Allah ka gafarta mini, Mai Shari’a, ina roƙon jinƙai, yallabai. Ba zan sake aikata wani laifi ba.” Inji Babangida.

Daga nan ne alkalin kotun yankin, Saminu Suleiman, ya baiwa wanda ake tuhuma zabin tarar naira 6,000, inda ya gargade shi da ya daina aikata laifin bayan kammala hukuncin da aka yanke musu.

Tun da farko, mai gabatar da kara, Mista Chinedu Ogada, ya shaida wa kotun cewa a ranar 11 ga watan Nuwamba mai shigar da kara Usman Zaiyanu na Junction Tumatir Zuba Abuja ya kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Zuba.

More from this stream

Recomended