Kotu ta yi watsi da ƙarar Binani, ta tabbatar da Fintiri a matsayin halattaccen gwamnan Adamawa

Kotun daukaka kara da ke Abuja a ranar Litinin ta yi watsi da karar da jam’iyyar APC da ‘yar takarar gwamna, Sanata Aisha Dahiru Binani, suka shigar na neman a soke zaben Umar Ahmadu Fintiri a matsayin zababben gwamnan jihar Adamawa.

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da hukuncin kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Adamawa wacce tun farko ta ayyana Gwamna Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukuncin da Mai Shari’a Tunde Oyebanji Awotoye ya rubuta ya yi watsi da shari’ar Binani da APC bisa wasu dalilai na rashin ka hankali.

Daga cikin dalilan, Kotun daukaka kara ta bayyana cewa Binani da APC sun kasa kiran wakilan zabe da suka halarci zaben a matsayin shedu amma abin takaici sun kira ko’odinetoci na yakin neman zabe wadanda ba sa nan a wurin zaben.

More from this stream

Recomended