Wata babbar kotu a jihar Kano ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar wato KANSIEC da ta cigaba da shirye-shiryen gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi da aka shirya gudanarwa ranar Asabar.
Alƙalin kotun, Sanusi Ado Maaji ya yanke hukuncin cewa kundin tsarin mulki ya bawa hukumar KANSIEC damar shiryawa tare da gudanar da zaɓen a dukkanin ƙananan hukumomin dake Kano.
An zartar da hukuncin ne a ranar Juma’a biyo bayan buƙatar gaggawa da hukumar zaɓen ta gabatar a gaban kotun.
Waɗanda ake ƙara a shari’ar sun haɗa da jam’iyyun Accord Party, Action Alliance, Action Democratic Party, African Democratic Congress, All Progressives Congress (APC), Allied Peoples Movement, All Progressive Grand Alliance, Boot Party da kuma Labour Party.
Sauran hun haɗa da National Rescue Movement, New Nigeria Peoples Party, Peoples Democratic Party (PDP), Peoples Redemption Party, Social Democratic Party, Young Progressive Party, Young Party da kuma Zenith Labour Party.
Alƙalin ya umarci jami’an tsaro da su samar da tsaron rayuka da kuma dukiya a yayin zaɓen.