Kotu ta bada umarni a ƙwace dala miliyan $2 daga wurin Emefiele

Babban kotun tarayya dake Lagos ta bayar da  umarnin wucin gadi na ƙwace zunzurutun kuɗi har dala miliyan $2.045 da wasu gine-gine bakwai da kuma hannayen jari mallakin, Godwin Emefiele tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya wato CBN.

Akintayo Aluko alƙalin kotun shi ne ya bada umarnin a ranar Alhamis  bayan da babban lauya Rotimi Oyedepo dake wakiltar hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta’annati ya gabatar gaban kotun kan ƙarar mai lamba FHC/L/MISC/500/24.

Oyedepo ya ce abubuwan da za a ƙwace akwai ƙwararan hujjoji dake nuna an same su ta haramtacciyar hanya.

Ya ƙara da cewa  a lokacin da ake gudanar da bincike an gano cewa tsohon gwamnan babban bankin ya nemi a bashi na goro kafin ya amince a  bawa wasu kamfanoni da ƴan kasuwa  dalar Amurka duk da cewa sun cika ka’idoji.

Lauyan na EFCC  ya nemi a miƙawa gwamnatin tarayya dukkanin kadarorin.

Da yake yanke hukuncin alƙalin kotun ya nemi a wallafa bayanan kadarorin a jaridu domin bawa duk wanda yake da ƙorafi damar bayyana a gaban kotun domin bada hujjar dalilin da zai sa baza a iya damƙawa gwamnatin tarayya kadarorin na din-din ba.

More from this stream

Recomended