Kano: An gurfanar da wanda ya daɓa wa abokinsa wuƙa har lahira a gaban kotu

Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da wani Musbahu Ya’u a gaban babbar kotun jihar mai lamba 14 da ke zaune a titin Miller Road da laifin daba wa abokinsa wuka a ciki.

Ana tuhumarsa ne da laifin dabawa Kamalu Sadik wuka har sai da huhunsa ya fito bayan an samu rigima a tsakaninsu.

Lokacin da mai gabatar da kara, Barista Lamido Abba Sorondinki, ya karanta masa tuhumar da ake masa, Yau ya musanta tuhumar.

Saboda haka, Sorondinki ya roki kotu da ta dage shari’ar don ba su damar kawo shaidunsu.

Lauyan wanda ake kara, Barista Ahmad Ali, bai ki amincewa da rokon l da lauyan masu gabatar da kara ya yi ba, sai dai ya bukaci kotun da ta umurci masu kara da su ba su takardun da za a gabatar a gaban kotu.

Don haka alkalin kotun ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Fabrairun 2024.

More from this stream

Recomended