Kano: An gurfanar da wanda ya daɓa wa abokinsa wuƙa har lahira a gaban kotu

Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da wani Musbahu Ya’u a gaban babbar kotun jihar mai lamba 14 da ke zaune a titin Miller Road da laifin daba wa abokinsa wuka a ciki.

Ana tuhumarsa ne da laifin dabawa Kamalu Sadik wuka har sai da huhunsa ya fito bayan an samu rigima a tsakaninsu.

Lokacin da mai gabatar da kara, Barista Lamido Abba Sorondinki, ya karanta masa tuhumar da ake masa, Yau ya musanta tuhumar.

Saboda haka, Sorondinki ya roki kotu da ta dage shari’ar don ba su damar kawo shaidunsu.

Lauyan wanda ake kara, Barista Ahmad Ali, bai ki amincewa da rokon l da lauyan masu gabatar da kara ya yi ba, sai dai ya bukaci kotun da ta umurci masu kara da su ba su takardun da za a gabatar a gaban kotu.

Don haka alkalin kotun ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Fabrairun 2024.

More News

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Wasu ɗaliban Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a lokacin turmutsutsin karɓar tallafin abinci

Dalibai biyu daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya barke a lokacin da suke kokarin...

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...

Miyetti Allah ta nemi a cafke Sunday Igboho saboda barazanar yaƙar Fulani

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, ta yi kira da a damke wani dan kabilar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi...