Jami’an Tsaro Sun Kuɓutar Da Mutane 58 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Kogi

Ƴan Sanda sun ce to mutane 58 da aka yi garkuwa da su a Dajin Udulu dake karamar hukumar Gegu ta jihar Kogi, dajin na Ubulu ya haɗa iyaka da Dajin Sardauna dake jihar Nasarawa da kuma wasu wurare da aka tabbatar matattarar masu garkuwa da mutane ce dake garuruwan dake makotaka da birnin tarayya Abuja.

Amma kuma ɗaya daga cikin mutanen da aka kuɓutar mai suna Tama Jonathan ya mutu sakamakon raunin da ya samu lokacin da ake kokarin ceto su.

An kuma miƙa gawarsa ga iyalansa yayin da sauran wadanda aka ceto aka kai su asibiti kuma za a mika su ga iyalansu.

Sanarwar rundunar yan sandan ta ce yan bindigar sun buɗe wuta sa’ilin da suka hangi jami’an tsaro abin da ya sa suma suka mayar da martani.

More from this stream

Recomended