INEC ta ki sauya matsaya kan rikicin APC a Zamfara

Shugaban hukumar zaben Najeriya

Hakkin mallakar hoto
@INECNIGERIA

Image caption

Hukumar zaben Najeriya ta bayyana cewa har yanzu ba ta yanke shawara a kan wata wasikar da ministan shari`ar kasar ya aika mata ba kan rikicin APC a Zamfara.

Wata wasika da ta dinga yawo a kafofin sadarwa na intanet mai dauke da sa hannun Ministan shari’ar kasar ta bukaci hukumar da ta duba yiwuwar bai wa jam`iiyar APC damar mika `yan takararta na mukamin gwamna da `yan majalisun tarayya na jihar Zamfara, domin fafatawa a zaben 2019.

Ministan shari`ar, Abubakar Malami ya mika wannan bukatar ne ga INEC inda ya kafa hujja da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, hukuncin da ya ce ya ba wa hukumar zabe damar karbar `yan takara daga jam`iyyar APC ta jihar Zamfara.

Amma mai magana da yawun hukumar zaben, Mallam Aliyu Bello ya shaida wa BBC cewa INEC ba ta cimma matsaya a kan wasikar ba, sai sun kammala nazari.

“Komi girman takarda da kuma inda ta fito, sai INEC ta tsaya ta yi nazari kuma ta diba matakin doka kafin daukar matakin da ya dace da bai saba ka’idojinta ba.”

INEC tana daukar mataki na kashin kanta ne ba umurnin da bai fito daga kotu ba,” in ji shi.

Malam Aliyu ya ce duk da ba ya da labari ko masaniyar takardar ta zo hannun INEC amma idan ma har sun karbi takardar to sai INEC ta zauna ta yi nazari ta diba muhallin takardar ta kuma ikonta da inda ta fito.

Ya kara jaddada cewa matsayin hukumar zabe na baya na nan bai canza ba, “wato jam’iyyar APC ba ta dan takara a jihar Zamfara a matsayin zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha da na tarayya.”

Ya ce idan akwai wani abu da ya fito daga baya, INEC za ta fito ta yi bayani.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...