INEC ta dakatar da Kwamishinanta na Adamawa

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta dakatar da Kwamishinan Zabe na Adamawa Hudu Yunusa Ari.Wannan matakin na zuwa ne bayan sanarwar da Kwamishinan ya yi a ranar Lahadin da ta gabata bayan zaben da aka gudanar a Adamawa.Ari ya ayyana Aisha Dahiru Binani ta jam’iyyar All Progressives Congress, APC, a matsayin wadda ta lashe zaben duk da cewa jami’an tattara sakamakon zabe ne kadai aka ba su izinin yin hakan.Wata wasika da ta fito 17 ga Afrilu, 2023, mai dauke da sa hannun Sakatariyar INEC, Rose Oriaran-Anthony, ta sanar da dakatar da Ari tare da umurtar Sakataren Gudanarwa na Adamawa ya maye gurbinsa.

More News

Sojojin Nijeriya sun hallaka ‘yan ta’adda 191 tare da kama 184

Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana hakan ne a wata sanarwa wacce aka fitar bayan wani taron manema labarai da rundunar ta yi a Abuja...

Wani wanda ya gama jami’a ya yi yunkurin kashe kansa saboda rashin ba shi satifiket ɗinsa

Wani wanda ya kammala karatun digiri a jami’ar Ambrose Ali da ke Ekpoma a jihar Edo mai suna Precious Ogbeide ya yi yunkurin kashe...

Google yana bikin cika shekaru 25 da kafuwa

A yau ne kamfanin fasaha na Google yake bikin cika shekaru 25 kafuwa. Sergey Brin da Larry Page suka samar da shi a cikin watan...

An ceto ɗaliban jami’ar Zamfara guda 14 da ƴan bindiga suka sace

Jami'ar Tarayya ta Gusau da ke jihar Zamfara ta bayar da sanarwar cewa ya zuwa yanzu an ceto ɗalibai 14 da leburori biyu waɗanda...