Harin sojan saman Najeriya ya yashe Ba’a Shuwa jagoran ƙungiyar ISWAP a Najeriya

Rundunar sojan Najeriya ta samu nasarar kashe shugaban kungiyar yan ta’addar ISWAP a Najeriya, Baa Shuwa tare da wasu daga cikin mayaƙan kungiyar a jihar Borno a yayin wani farmaki da aka kai masa.

Ba’a Shuwa shi ne shugaban kungiyar ta ISWAP dake biyayya ga kungiyar ISIS a yankin tafkin Chadi, Kwalfarji, Timbuktu Faruq da Sambisa Mantika.

Tun bayan mutuwar Abubakar Shekau jagoran kungiyar ta ISWAP, Ba’a ya maye gurbinsa.

Majiyoyin sirri na jami’an tsaro sun faɗawa Zagazola Makama masanin tsaro dake wallafa bayanai a yankin tafkin Chadi cewa an kai harin da ya kashe Ba’a Shuwa tare wasu mayaƙansa ranar 2 ga watan Janairu 2024 a Kwatan Dilla dake karamar hukumar Abadam ta jihar Borno.

Majiyoyin sun bayyana cewa hoton da aka dauka bayan harin ya nuna gawarwaki da dama a wurin.

More from this stream

Recomended