Gwamnatin Lagos Ta Samar Da Manyan Motocin Fasinja Masu Amfani Da Lantarki

Gwamnatin jihar Lagos ta karbi rukunin farko na manyan motocin fasinja dake amfani da wutar lantarki domin jigilar al’ummar jihar.

Gwamnan jihar Babajide Sanwoolu shi ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Da yake magana kan amfanin motocin Sanwoolu ya ce motocin za su rage samar da hayakin dake gurbata muhalli kuma al’ummar jihar za su amfana da sufuri mai rahusa.

Gwamnan na Lagos ya ce an cimma wannan nasara ne sakamakon hadin gwiwa da gwamnatin jihar ta shiga da kamfanin Wando Clean Energy Limited.

More from this stream

Recomended