
Sojojin Najeriya dake aiki a bataliya ta 51 dake Banki sun kashe mayakan Boko Haram da dama a jihar Borno.
A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan harkar tsaro a yankin tafkin Chadi an kai farmakin ne a ranar Juma’a tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron Civilian JTF.
Bayanan da aka wallafa sun bayyana cewa sojojin sun kai farmaki ne a maboyar yan ta’addan dake Gargash a karamar hukumar Bama ta jihar.
An jiyo wata majiya dake randunar sojan Najeriya na cewa yan ta’addar na shirin kai hari ne lokacin da sojoji suka kashe su.
Ma’aikatan agaji biyu da aka sace a Monguno a cikin shekarar 2022 aka ceto a yayin artabun da aka yi da yan ta’addan.