Gwamnatin jihar Katsina ta sassauta dokar hana fita da aka saka a jihar.
Dokar hana fitar da ta taƙaita zirga-zirga daga ƙarfe 07:00 na dare ya zuwa 07:00 na safe a yanzu an sassauta ta ya zuwa 10:00 na dare zuwa 10:00 na safe a dukkanin faɗin jihar .
Sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Garba Faskari ya sanar cewa mataimakin gwamnan jihar kuma mai riÆ™on muÆ™amin gwamnan jihr Mallam Faruk Lawal Jobe ya gamsu da rahotanni da yake samu na ingantar yanayin tsaro a ko’ina cikin jihar saboda haka ya bayar da umarnin rage wa’adin dokar ba tare da É“ata lokaci ba.
Mai riÆ™on muÆ™amin gwamnan ya yabawa jami’an tsaro yadda suka gudanar da aikinsu da kuma al’ummar gari ta yadda suka bada haÉ—in kai har gwamnatin ta shawo kan lamarin.