Gwamnati za ta fara biyan ma’aikata naira 30,000 mafi Ć™arancin albashi a Zamfara


Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya sanar da cewa za su fara aiwatar da tsarin mafi Ć™arancin albashi naira 30,000 ga ma’aikatan jihar daga farkon watan Yuni mai zuwa.

Gwamnan ya faɗi hakan ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin ƙungiyar ƴan ƙwadago reshen jihar.

Tun da farko dai Ć™ungiyar Ć™wadago ta Ć™asa reshen jihar Zamfara ta bai wa gwamnatin jihar wa’adi zuwa ranar 23 ga watan Mayu ta fara aiwatar da mafi Ć™arancin albashin, tare da barazanar shiga yajin aiki matuĆ™ar aka gaza cimma matsaya.

More News

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Wasu É—aliban Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a lokacin turmutsutsin karÉ“ar tallafin abinci

Dalibai biyu daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya barke a lokacin da suke kokarin...

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...

Miyetti Allah ta nemi a cafke Sunday Igboho saboda barazanar yaƙar Fulani

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, ta yi kira da a damke wani dan kabilar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi...