Gwamnan Legas Sanwo-Olu ya kara mafi ƙarancin albashi zuwa naira 85,000

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana shirin gwamnatinsa na fara biyan sabon mafi karancin albashi na N85,000 ga ma’aikatan jihar.

Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake halartar shirin Politics Today, wani shiri na tattaunawa a tashar Channels TV.

“Ina farin cikin sanar da ku cewa mafi karancin albashi a Jihar Legas, wanda muka tattauna da kungiyarmu, yanzu ya zama N85,000,” in ji Sanwo-Olu, yayin da yake amsa tambayar da mai gabatar da shirin ya yi masa kan batun mafi karancin albashi.

Gwamnan ya bayyana cewa wannan adadin ba gasa ba ce da sauran jihohi, amma la’akari ne da ikon jihar wajen biyan albashin.

More from this stream

Recomended