Firaministan Canada na tsaka-mai-wuya saboda tsohon hotonsa | BBC Hausa

Justin Trudeau da abokanan aikinsa a lokacin
Hakkin mallakar hoto
TIME MAGAZINE
Image caption

Tsohon hoton da ya jefa Firaministan na Canada cikin tasku kenan, inda ya yi shiga a matsayin bakar fata da kayan Larabawa

Firaministan Canada, Justin Trudeau yana ta faman mayar da martani da neman gafara kan wani rahoto da aka yi wanda ke nuna wani tsohon hotonsa, ya shafa launi na bakar fata da yin shiga ta Larabawa, saboda ana daukar hakan kamar wariyar launi ce.

A hoton Mista Trudeau ya shafa launi irin na bakaken fata a fuska da hannusa, ya kuma sanya rawani da jallabiya har da falmaran a jikinsa, inda yayi shiga ta tamkar bakin Balarabe, a lokacin wata liyafa a wata makaranta da yake koyarwa shekara 18 da ta wuce.

Mujallar Time Magazaine ce ta wallafa hoton wanda yanzu ya jawo ana ta zargin Firaministan da shiga ta cin zarafi da nuna wariyar launin fata.

Hakkin mallakar hoto
Others
Image caption

Justin Trudeau ya ce ya kamata a ce na fahimci illar abin a lokacin, amma ban farga ba sai yanzu

Shi dai wannan tsohon hoto, wanda ke neman sa farin jinin Firaministan da ke fuskantar neman sake zabensa, ya dusashe, tsohon malamin makarantar ya dauke shi a lokacin wata liyafa a makarantar, liyafa ta yin al’adun Larabawa, da ake kira Arabian Night.

Firaminista Justin Trudeau ya dauki hoton ne a makarantar mai zaman kanta a birnin Vancouver a lokacin.

Ya ce shi da dai bai taba tunanin za a dauki wannan shiga da ya yi a matsayin ta kwaikwayo domin muzantawa ko wariyar launin fata ba, amma ya ce a yanzu ya farga da hakan.

Firaministan dan siyasa ne da a cikin tsanaki ya sama wa kansa suna da farin jini a matsayin wanda ke da kishi kuma jagora mai kare kabilu da jinsi na marassa rinjaye a Canada.

Dan siyasa ne na wannan zamani na shafukan sada zumunta, wanda ke jagorantar jamiyyar Liberal Party wadda ta yi suna a kan akidunta na kawo sauyi kan batutuwa da suka kama daga daidaito tsakanin maza da mata zuwa ga tabbatar da ‘yanci.

A makon da ya wuce ne ya kaddamar da takararsa ta neman a sake zabensa, inda har alkaluma suka nuna yana gaba da babban abokin hamayyarsa.

Yanzu dai a wannan zabe da ake ganin zai ja hankali saboda za a fatata sosai, ana ganin bayyanar wannan hoto ka iya yi masa nakasu, wanda tuni ‘yan hamayya da masu raji ke ta caccakarsa.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...