Farashin mai ya tashi bayan harin Iran kan sojin Amurka | BBC News

Flames rising from the burning of excess hydrocarbons at the Nahr Bin Omar natural gas field, north of the southern Iraqi port of Basra.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Farashin danyen mai ya tashi bayan da wasu makmai masu linzami suka afkawa wasu sansanonin sojojin Amurka biyu da ke Iraki.

Farashin danyen mai samfurin Brent ya tashi da kashi 1.4 cikin 100 inda ake sayarwa kan $69.21 kowace gangar mai daya a kasuwar mai ta Asia.

Su ma ma’adinan kasa kamar gwal da kudin Japan Yen sun tashi bayan da aka kai harin.

Kazalika hannun jari a duniya ya yi kasa sakamakon rikicin da ake yi a yankin gabas ta tsakiya.

Kasuwar hannayen jari ta Japan, Nikkei 225 ta yi kasa da kashi 1.3 cikin 100 yayin da kasuwar hannayen jari a Hong Kong, Hang Seng ta yi kasa da kashi 0.8 cikin 100.

Kafar talabijin ta Iran ta ce harin ramuwar gayya ce kan kisan Babban Kwamandan kasar Qasem Soleimani.

Harin ya faru ne sa’oi bayan jana’izar Soleimani wanda ya mutu sakamakon harin da jiragen Amurka mara matuka suka kai ranar Juma’a.

Mutuwarsa dai ta haifar da fargabar cewa rikici tsakanin Amurka da Iran na iya ta’azzara.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...