
Sanata da ya wakilci al’ummar mazabar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa ta 8 ya shawarci yan arewa da su goyi bayan yankin kudu maso yamma a 2027 domin su kammala shekara mulki na tsawon shekaru 8.
Ya soki shugabanni yan arewa da suka rike madafun iko amma suka gaza kawo cigaba da bunkasa tattalin arzikin yankin a tsawon shekaru.
Da yake wa yan jaridu jawabi a gidansa dake Kaduna Shehu ya ce Arewa ta yaba da cigaban da aka samu kawo yanzu a karkashin gwamnatin shugaba, Bola Ahmad Tinubu inda shawarci mutane da su goyi bayan shugaban kasar a 2027.
” Ga wasu daga cikin da suka fito daga wannan yanki(Arewa) na kasarnan mun yaba da cigaban da wannan gwamnati ta kawo ya zuwa yanzu a wurin wasu da suka samu damar su yi fiye da haka amma suka gaza muna fada musu ya fi ace sun bayar da hakuri kan kuskuren da suka yi wa al’ummar arewa,” ya ce.
” Ga talakawan arewa kada su bari a tunzura su su tsani gwamnatin da take ayyukan alkhairi sosai fiye da ta wadanda suka fito daga yankin,”
Ya ce abu mafi a ala shi ne arewa ta kyale kudu tayi mulki na tsawon shekaru 8.