Connect with us

Hausa

Dagaske an fara wahalar mai a Najeriya? – BBC Hausa

Station wey dey sell petrol for Port Harcourt

Hukumar da ke kula da albarkatun man fetur a Najeriya DPR ta bayyana cewa ta yi mamaki bisa yadda wasu daga cikin gidajen mai a kasar ke nuna cewa ana wahalar mai a kasar amma gidajen man sun san cewa suna da mai cike a rumbunansu.

Hukumar ta shaidawa BBC a ranar Asabar cewa a jihar Legas kadai, an kai litar mai kusan miliyan 60 kuma hukumar ta bayyana cewa akwai jami’anta da suka zagaya wasu gidajen mai da ke Legas kuma sun ce ana sayar da mai lami lafiya ba tare da wata matsala ba.

Sai dai daya daga cikin shugabannin hukumar Wole Akinyo ya shaidawa BBC cewa ” A cikin birnin Legas mun gano cewa jama’a na yada jita-jita bisa cewar ana wahalar mai, hakan na jawo fargaba har mutane su yi tururuwa zuwa gidajen mai, amma idan muka je gidajen mai zagaye sai muga alama kamar ana wahalar mai amma akwai mai, tsoro ne kawai da aka ba mutane.”

Ya bayyana cewa akwai wasu gidajen mai da suna da kusan lita dubu 35 a rumbunansu amma sai su rinka amfani da famfo daya ko biyu suna sayar da mai wanda hakan na jawo dogon layi da zai gigita mutane su yi zaton kamar akwai wahalar mai.

Ya ce ”da dama wasu gidajen mai su ke kirkiro wahalar mai domin wasu gidajen na da famfon sayar da mai goma amma sai su yi amfani da biyu.”

Fatakwal

A jihar Fatakwal da ke kudu maso kudancin Najeriya, hukumar da ke kula da albarkatun man fetur din ta bayyana cewa wannan jita-jitar da ake yadawa bata yi wani tasiri ba a jihar domin a zagayen da suka yi, kusan ko wane gidan mai na sayar da mai ba tare da wata matsala ba.

Image caption

Babu alamun wahalar mai a jihar Kano

Kano

A jihar Kano da ke arewacin Najeriya, jama’a na ci gaba da zirga-zirgarsu sakamakon jita-jitar da ake yadawa ta wahalar man fetur ba ta yi tasiri ba.

BBC ta ziyarci wasu unguwanni da ke da dumbin gidajen mai a jihar, amma babu alamun layi sakamakon duka gidajen man na sayar da mai kamar yadda suka saba.

BBC ta tattauna da wani matafiyi da ya zo halartar daurin aure a Kano a ranar Asabar inda ya bayyana cewa bai ga wani dogon layi ba ko kuma alamun fargabar wahalar mai a jihar.

Abuja

A babban birnin tarayyar kasar, BBC ta gano cewa babu layin mai a wasu wurare amma wasu wuraren kuma tuni aka fara dogon layin mai.

Hakkin mallakar hoto
Kingsley Amajiri

Babu wahalar mai a Najeriya- Hukumar NNPC

Kamfanin man fetur na Najeriya NNPC ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa ana wahalar man fetur a kasar.

Manajan rukunin kamfanin mai kula da yada labarai Ndu Ughamadu ya bayyana cewa marasa tunani ne ke yada irin wannan jita-jitar.

Hukumar ta bayyana cewa jama’a su daina damuwa sakamakon akwai isashen man fetur da ya kai sama da lita biliyan 1 a watan Afrilun 2019.

Facebook Comments
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Masu zanga-zanga sun yi galaba kan soja a Sudan

Zanga-zangar Sudan

Wasu jiga-jigan gwamnatin mulkin soja su uku a Sudan sun mika tayin sauka daga kan mukamansu- wata muhimmiyar bukata ce ta masu zanga-zanga a kasar.

Ana kallon manyan janar-janar din a matsayin manyan na-hannun daman tsohon shugaba Omar al-Bashir.

Matakin ya zo ne bayan tattaunawa tsakanin sojoji da jam’iyyun adawa kan yadda za a kafa gwamnatin farar hula.

A wani taron manema labarai, kakakin rundunar sojan kasar Laftanar Janar Shamseddine Kabbashi ya ce bangarorin biyu sun cimma matsaya kan mafi yawan bukatun kuma sun yanke shawarar kafa kwamitin hadin gwiwa don warware duk wasu matsaloli.

Jagororin zanga-zanga a Sudan din sun kira wani maci na mutum miliyan daya a yau Alhamis domin matsawa majalisar koli ta sojan kasar mika mulki ga gwamnatin farar hulla.

Jiragen kasa makare da mutane na isa Khartoum, babban birnin kasar don shiga gangamin da za a yi a wajen shelkwatar rundunar soji.

A karon farko, alkalai sun bayyana cewa za su shiga zanga-zangar don nuna goyon bayansu, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

An yi jana’izar mutum 19 a Jigawa

FRSC

An yi jana’izar mutum 19 da suka mutu sanadiyyar wani hadarin mota a karamar hukumar Gwaram da ke jihar Jigawa ranar Laraba.

Hadarin ya faru ne a garin Gwaram Sabuwa da misalin karfe 11:30 na dare, bayan da tayar gaban motar da ke dauke da fasinjoji 40 ta fashe.

Rahotanni sun ce daga nan ne sai motar ta wuntsula kafin ta kama da wuta. Mutum 21 daga cikin fasinjojin ne dai suka ji rauni.

Wani da abin ya faru a kan idonsa ya ce gawarwakin fasinjojin sun kone “kurumus ta yadda ba za a iya gane su ba.”

“Na ga gawarwakin jarirai shida tare da gawarwakin iyayensu,” in ji shi.

Mutanen da hadarin ya rutsa da su wadanda galibinsu mata ne da kananan yara suna kan hanyarsu ta dawowa daga daurin aure ne.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Zaman fursuna na shekara 3 ko tarar $3,000 ga masu shan shisha

shisha

Wuraren da ake shan tabar shisha a Ghana za su dinga fuskantar hukunci mai tsanani idan har ba su bi dokokin kiyaye lafiya da kasar ta tanadar ba.

Shan tabar Shisha dai ya zama ruwan dare a tsakanin matasa a kasar.

Sai dai akwai sabanin ra’ayi kan cewa tabar shisha ba ta da illa kamar taba sigari.

Amma Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO da Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Ghana FDA, ba su yarda da wannan batu ba.

Hukumar ta ce daga yanzu duk mai mashayar da aka kama ana shan shisha a wajen zai fuskanci zaman gidan yari na shekara uku ko a ci shi tarar dala dubu uku, kwatankwacin naira miliyan daya da 80,000 kenan.

Sai dai wannan hukunci zai hau kansu ne kawai idan ba su yi rijistar shishar ba ko kuma idan ba su sanya sanarwar gargadi kan irin hadarin da ke tattare da shanta yake ba.

Yayin shan shisha

Shan wannan taba mai kanshin gaske na kara karbuwa a wurin jama’a a fadin duniya, amma masana harkar lafiya sun ce mafi yawan wadanda suke shanta ba su san hadarin da ke tattare da hakan ba.

Yanzu dai mutane ne da dama suke cin moriyar wannan taba wadda ke tashe a Indiya da Gabas ta tsakiya inda aka ce daga nan ta samo asali.

A Gabas ta tsakiya yayin ya ratsa har tsakanin ‘yan yara maza da mata da ma manyan mata wadanda yawancinsu ba sa shan taba.

Wannan yayi yanzu ya kai har ga kasashen Turai da Brazil da kuma Amurka inda za ka ga shagunan shan wannan taba mai zamani.

Shugaban sashen tiyatar zuciya a babban asibitin kasa na Saudi Arabia, National Guard Health Affairs, Farfesa Hani Najm, ya taba sheda wa BBC a wata tattaunawa cewa yana fargaba shan tabar shisha zai iya kara yawan masu cutukan zuciya a kasashen yankin Gabas ta tsakiya.
Facebook Comments
Continue Reading
Advertisement
Advertisement

Trending

%d bloggers like this: