Buhari ya umarci ministocinsa dake son yin takara su ajiye aikinsu

Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya umarci ministocin gwamnatinsa da suke da shaawar tsayawa takar to su sauka daga kan mukaminsu kafin nan da ranar Litinin.

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Muhammad shi ne ya bayyana haka lokacin da yake wa manema labarai jawabi kan abin da aka tattauna a taron majalisar zartarwa ta tarayya na ranar Laraba.

Akwai dai ministoci da dama da suka nuna shaawarsu ta yin takarar mukamai daban-daban kama daga shugaban kasa da kuma kujerar gwamna.

More News

Hoto:Kwankwaso Ya kaddamar da wasu ayyuka a Kaduna

Biyo bayan gayyatar da gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya yi masa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya kaddamar da wasu...

Sarkin Kano Aminu Ado ya zama uba ga Jami’ar Calabar

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya samu girmamawa bayan an nada shi a matsayin uban Jami'ar Calabar da ke Jihar Cross...

Za a yi Ruwan Sama a Wasu Garuruwan Adamawa —Mai hasashe

Wani mai hasashen yanayi a Najeriya Alhaji Adamu Katakore ya faɗa cewa za yau Alhamis za a samu ruwan sama a wasu garuruwan jihar...