Bayani kan rayuwar Shugaba Muhammadu Buhari

Muhammadu Buhari

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Muhammadu Buhari mai shekara 76 – mutum ne da ake ganinsa a matsayin tsayayye wanda ba ya gudu ba ja da baya.

Duk da shan kaye da ya yi a zabuka uku da suka gabata, amma ya sami nasara a zaben 28 ga watan Maris din 2015, inda ya zama dan adawa na farko da ya sami galaba a kan shugaban da ke kan karagar mulki.

Buhari ya kara da Shugaba Goodluck Jonathan, wanda dan yankin Neja Delta ne, a karo na biyu da gudanar da zaben.

A wannan karon ya yi sa’ar samun goyon bayan gamayyar jam’iyyun siyasar Najeriya mai suna All Progressives Congress (wato APC).

 • Buhari ba ya karya -Ministar kudi
 • Na zama ‘Baba go slow’ saboda dimokuradiyya – Buhari

Jam’iyyar APC ta sami karin karfi bayan da manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyar Shugaba Jonathan ta People’s Democratic Party (wato PDP) suka sauya sheka, jam’iyyar ta PDP ce ta mamaye fagen siyasar Najeriya tun karshen mulkin soji a shekarun 1999.

Sa rai da samun sauyi

Bayan da shugaban ya dare mulki a 2015, ‘yan Najeriya da dama sun saka rai da samun sauyin rayuwa, ta bangaren ingantuwar tsaro da tattalin arziki da magance cin hanci da rashawa.

Sai dai masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun sha cewa shugaban bai yi wani abin a zo a gani ba ta bangaren tattalin arziki.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Sai dai ana yaba masa ta wajen magance rikicin Boko Haram, duk da cewa suna ganin da sauran rina a kaba a wannan fannin ma.

A bangaren tattalin arziki kuwa, masu sharhi da dama suna ganin babu wani cigaba da aka samu, “sai ma kara tabarbarewa da yake yi.”

Rashin lafiya

Shugaba Buhari ya shafe tsawon lokaci yana jinya a shekarar 2017, inda har ya shafe sama da kwana 100 yana jinya a Birtaniya.

Wannan al’amari ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a ciki da wajen kasar.

A lokacin da rudani ya yawaita kan halin da shugaban ke ciki da kuma rashin jin ta bakin makusantansa game da ainiyin abin da ke damun shugaban.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

‘Yunkurin kisa’

Buhari mutum ne mai farin jini a wajen talakawa a yankin arewacin kasar.

An yi zaton zaman Buhari tsohon janar na soja, kana sanin halinsa na bin doka da oda zai ba kasar damar fuskantar kalubalen ta’adancin masu kaifin kishin Islama da suka mamaye yankin arewa maso gabashin kasar.

Shi dai Musulmi ne daga Daura a jihar Katsina, kuma tuni ya bayar da goyon bayansa ga tsarin aiwatar da shari’a a arewa, wanda ya sanya a baya dole ya fito yana kare kansa daga zargin da ake masa na cewa shi mai tsatsaurin ra’ayin addini ne.

Fiye da mutum miliyan uku ne rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a arewa maso gabashin kasar

Hakan ya yi masa illa a lokacin zaben shekarar 2003 – lokacin da ya kasa samun goyon bayan Kiristoci da ke kudancin kasar.

Amma bayan da ya tsallake rijiya da baya a lokacin da aka kai hari kan jerin motocin da ke masa rakiya a Kaduna, harin da ya yi kama da irin wanda kungiyar Boko Haram take kai wa na kisan wadanda ke adawa da ita, Buhari ya yi alkawarin kawo karshen ta’addanci cikin watanni idan aka zabe shi.

Sai dai har yanzu rikicin Boko Haram yana ci gaba da zama kalubale a kasar, musamman a ‘yan watannin nan.

Shugaba Buhari ya taba alakanta rashin karfin halin shugaba Jonathan a dalilin da ya jawo tabarbarewar al’amarin, da kuma kin yarda da kiraye-kirayen da ake masa na ya hau teburin tattaunawa da kungiyar.

Har yanzu ana tuna shi da matakan da ya dauka a lokacin yana kwamandan sojin Najeriya a shekarar 1983 – lokacin da wasu sojiojin Chadi suka kwace wasu tsibirai mallakin Najeriya – a yankin arewa-maso-gabas, yankin da sojojin kasar ke rike da shi bayan da ya fatattaki masu harin.

“Yaki Da Rashin Da’a”

Ya mulki Najeriya daga watan Janairu na 1984 har zuwa watan Agusta na 1985, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Disamba na 1983.

Wannan lokaci ne da ake tunawa da shi don tsananin aiwatar da yaki da rashin da’a da kuma take hakkin dan Adam da gwamnatinsa ta yi.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

 • Shin Buhari na samun nasara a yaki da cin hanci?
 • Matar da ta ‘damfari’ mutane a fadar Shugaba Buhari

Bayani kan Shugaba Muhammadu Buhari a takaice:

 • Shekararsa 76
 • An zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 28 ga Maris 2015
 • Ya yi shugaban mulkin sojan Najeriya daga 1984 zuwa 1985
 • An hambare shi a juyin mulki
 • An yi amanna ba shi da cin hanci da rashawa
 • Mai ladabtarwa ne – a kan sa ma’aikatan gwamnati tsallen kwado idan suka makara zuwa aiki
 • Musulmi ne daga arewacin Najeriya
 • Ya tsallake rijiya da baya a wani hari da Boko Haram ta kai masa.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Akwai bambamcin ra’ayi game da tasirin mulkin sojin Buhari na watanni 20 da ya yi.

Kimanin ‘yan siyasa 500 da ma’aikata da ‘yan kasuwa ne aka tsare a kurkuku a lokacin wannan yaki na almubazzaranci da cin hanci da rashawa.

Wasu mutane suna ganin hakan a matsayin yin amfani da karfin soji da ya wuce misali.

Wasu ko suna tuna wannan lokacin a matsayin wani yunkurin yaki da cin hanci da yaki ci yaki cinyewa, abin da ya dakile ci gaban Najeriya.

A dalilin wannan ne ‘yan siyasa har ma da sojoji da farar hula suka shaide shi da halin gaskiya da rikon amana.

 • Buhari ya damu da kashe sojojin Najeriya a Borno
 • Na fi Buhari yaki da cin hanci da rashawa — Jonathan

Daya daga cikin abubuwan da ya yi shi ne bai wa ‘yan Najeriya umarnin bin layuka a tasoshin shiga mota kana ya tura sojoji masu rike da bulala su sa ido.

An dinga ladabtar da ma’aikatan gwamnatin da aka kama su da zuwa wurin aiki a makare ta hanyar sanya su yin tsallen kwado.

A shekarar 2015 jam’iyyun adawa sun hada kai don ganin an kayar da PDP a zaben shugaban kasa.

Ya kuma gabatar da wata doka mai tsauri ta sanyawa ‘yancin ‘yan jarida takunkumi, inda har aka daure wasu ‘yan jarida biyu a lokacin mulkin sojansa.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

A hannu guda kuma, kokarinsa na farfado da tattalin arziki inda ya dakatar da shigo da kayayyaki daga kasashen waje ya jawo mutane da dama sun rasa ayyukan yi tare da durkushewar kasuwancinsu.

Farashin kayayyaki sun tashi inda rayuwa ta sauya, wanda hakan ya sanya Janar Ibrahim Babangida ya yi masa juyin mulki ranar 27 ga watan Agustan 1985. An daure Buhari a kurkuku na tsawon wata 40.

Janar Babangida ya so ya yi gaggawar bai wa farar hula mulki, wanda Janar Buhari bai dauki hakan da muhimmanci ba.

‘Mutane ya rage naku’

Janar Buhari ya ci gaba da kare dalilin da ya sa ya yi juyin mulki a ranar 31 ga watan Disambar 1983.

A watan Oktobar 2005 ne Janar Buhari ya ce, “Ya rage wa mutane. Idan kuna son shugabanci na gari, to ba bu bukatar mulkin soja.

“An samu mulkin soja ne a lokacin da ya zama dole ana bukatar hakan, kuma wadanda aka zaba na farar hular ba su yi abin a zo a gani ba.”

A lokacin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ke shugabanci na mulkin soja a shekarar 1970, Buhari ne ke rike da muhimmin mukamin ministan man fetur.

Amma dangantakarsu ta yi tsami bayan da Buhari ya hambare gwamnatin farar hula ta Alhaji Shehu Shagari, wanda shi ne ya ci zaben da Mista Obasanjo ya shirya.

Wannan ya ci gaba da jawo kace-nace game da matsayar Buhari dangane da demokuradiyya.

Obasanjo yana cikin mutanen da suka goya wa Buhari baya a zaben 2015, amma daga bisani tsohon shugaban ya soki manufofin Buhari kuma ma har ya ce ba ya goyon bayan tazarcensa a 2019.

Kafin shekarar 2015, Obasanjo wanda ya ci zaben shugaban kasa har sau biyu a karkashin inuwar jam’iyyar PDP daga 1999 ya ce:

“Buhari ba zai zama kwararren mai inganta tattalin arziki ba, amma zai zama shugaba mai karfin zuciya wanda ba za a iya tankwara shi ba, zai kuma kasance shugaba mara wasa da aiki.”

Hakkin mallakar hoto
INSTAGRAM/AISHA BUHARI

Image caption

Aisha Buhari ta sha sukar gwamnatin Mijinta

More News

Buhari names Semiu Adeniran new Statistician General of NBS

President Muhammadu Buhar has approved the appointment of Mr. Semiu Adeyemi Adeniran as the substantive Statistician-General of the Federation and Chief Executive Officer of...

2023: 7 APC aspirants battling for Oyo central senatorial district ticket

No fewer than seven aspirants on the platform of the All Progressives Congress (APC), have indicated interest to represent Oyo Central senatorial district in...

Kwankwaso ya ziyarci Obasanjo

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo. Ziyarar ta Kwankwaso wani bangare ne na cigaba da tattaunawar...

Kwankwaso ya ziyarci Obasanjo

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo. Ziyarar ta Kwankwaso wani bangare ne na cigaba da tattaunawar...