Atiku da mataimakinsa sun gana da Jonathan

0

Dantakarar shugaban kasa a jam’iyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da kuma mataimakinsa Ifeanyi Okowa sun ziyarci tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Atiku ya ziyarci Jonathan ne a gidansa dake Abuja.

Sanarwar ziyara na kunshe ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na soshiyal midiya.

Atiku Ya bayyana cewa sun tattauna da Jonathan ne kan yadda za a fafardo da Najeriya.