An Tsinci Gawar Wani Fitaccen Ɗandaudu A Abuja

An gano gawar wani fitaccen ɗan daudu mai shigar mata da ake kiransa da suna Abuja Area Mama a bakin kan babban titin Katampe – Mabushi dake Abuja a ranar Alhamis.

A wasu hotuna da suka karaɗe kafafen sadarwar zamani anga gawar ta sa a cikin jini duk jikinsa a karkace.

Hoton ya nuna fuskarsa tayi kaca-kaca a yayin da ƴan kayayyakin da yake ɗauke da su suke a watse a kusa da shi.

Benneth Igweh kwamishinan ƴan sandan birnin tarayya Abuja ya bayar da umarnin gudanar da bincike domin gano musabbabin mutuwar tasa.

Adeh ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa babu wata sheda da yake ɗauke da ita da za iya gane shi da ita.

More News

Jam’iyar PDP ta dakatar da Dino Melaye

Jam'iyar PDP a jihar Kogi ta dakatar da Dino Melaye tsohon ɗantakarar gwamna a jihar kan zargin cin amanar jam'iya. Shugabannin jam'iyar PDP na mazaɓar...

Sojoji sun kashe gawurtaccen ɗan bindiga Kachalla Buzu

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar kashe gawurtaccen ɗan bindiga Kachalla Halilu Sububu wanda aka fi sani da Kachalla Buzu. An kashe Kachalla ne...

Dakarun Najeriya sun hallaka ƴanbindiga a Neja

Rundunar sojin saman Najeriya ta hakala 'yanbindiga sama da 28 a yankin ƙaramar hukumar Shiroro dake jihar Neja.Wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai...

Tinubu ya gana da Sarki Charles

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga Sarki Charles na Birtaniya a fadar Buckingham a wata ziyara da yakai. Wannan ce ganawa...