Connect with us

Hausa

An sayi Iriyos naira dubu biyar, mafi tsada a Gano | BBC Hausa

Published

on

Ibrahim Iriyos

A farkon makon Satumba aka rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallon kafa ta nahiyar Turai, musammam Italiya da Faransa da Jamus da kuma Spaniya.

Sai dai tun ranar 8 ga watan Agusta aka rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan wasan ta Ingila.

A nahiyar Afirka akan gudanar da cinikayyar ‘yan kwallo sai dai kudin da ake sayen dan kwallo ku kusa ba ya kai wadanda ake yi a Turai.

Sai dai hakan bai hana saye da sayar da ‘yan wasan tamaula a nahiyar ba tun daga mataki na jiha da kananan hukumomi da yankuna da unguwanni.

Hakan ne ya sa aka gudanar da wani ciniki mafi tsada a Gano da ke karamar hukumar Dawakin Kudu a Najeriya, inda Super Stars ta dauki Ibrahim Salisu Iriyos a matsayin mafi tsada a garin.

Super Stars mai buga rukuni na biyu a gasar hukumar kwallon kafa ta jihar Kano ta sayo Ibrahin Iriyos daga Aston Villa ta Gano kan kudi naira dubu biyar daidai da fam 10.86.

Dan wasan mai cin kwallo shi da kansa ya yi sha’awar komawa Super Stars da murza leda ganin tana mataki na sama fiye da kungiyarsa ta Aston Villa Gano.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Idin Gano yadda ya ya cinikin Ibrahin Iriyos daga Aston Villa Gano

Hakan ya sa Iriyos kan je Super Stars atisaye a lokacin da kungiyarsa Aston Villa ke yin hutu, wanda hakan ya sa nan da nan aka amince da yadda yake taka leda aka kuma cimma matsaya a dauko shi.

Idin Gano shi ne shugaban Super Stars wanda ya je wajen kocin Aston Villa, Abba Alasan Isa wanda ake kira Abba Goma suka cimma matsaya kan farashin Ibrahim Iriyos.

Ga cinikayya da aka yi a manyan kasashen da suke kan gaba a tamaula a Turai a bana.

Gasar La Liga, Spaniya

An yi hada-hada 398 an kuma kashe sama da fan biliyan 1.70.

Wadanda aka saya mafi tsafa sun hada da:

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Joao Felix, dan wasan gaba, daga Benfica zuwa Atletico Madrid kan fan miliyan 113.

Antoine Griezmann, dan wasan gaba, daga Atletico Madrid zuwa Barcelona kan fan miliyan 107.6

Eden Hazard, dan wasan gaba, daga Chelsea zuwa Real Madrid kan fan miliyan 88.5

Gasar Serie A ta Italiya

An yi hada-hada 516 kan kudi fan biliyan 1.38

Wadanda aka saya mafi tsada:

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Romelu Lukaku, dan gaba, daga Manchester United zuwa Inter Milan kan fan miliyan 70

Matthijs de Ligt mai tsaron baya daga Ajax zuwa Juventus kan fan miliyan 67.8

Joao Cancelo mai tsaron baya daga Juventus zuwa Manchester City kan fam miliyan 60

Gasar Bundesliga, Jamus

An yi hada-hada 287 an kuma kashe fan miliyan 923.3

Wadanda aka saya mafi tsada:

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Lucas Hernandez mai tsaron baya daga Atletico Madrid zuwa Bayern Munich kan fan miliyan 68.

Luka Jovic, dan gaba, daga Eintracht Frankfurt zuwa Real Madrid kan fan miliyan 57.7

Sebastien Haller, dan gaba, daga Eintracht Frankfurt zuwa West Ham United kan fan miliyan 40.7

Gasar Premier, Ingila

An yi hada-hada 526 kan fan biliyan 1.83

Wadanda aka saya mafi tsada:

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Eden Hazard, dan gaba, daga Chelsea zuwa Real Madrid kan fan miliyan 88.5

Harry Maguire, mai tsaron baya, daga Leicester City zuwa Manchester United kan fan miliyan 80

Nicolas Pepe, mai buga gefe, daga Lille zuwa Arsenal kan fan miliyan 72

Facebook Comments
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Rikici tsakanin ‘yan Najeriya da Kenya a kan Lupita

Published

on

Lupita

Hakkin mallakar hoto
AFP

Fada ya kaure tsakanin ‘yan Najeriya da takakwarorinsu na kasar Kenya a shafin twitter saboda zabar wata jaruma ‘yar kasar Kenya, Lupita Nyong’o ta fito a matsayin ‘yar Najeriya a wani shirin fim.

Fim din mai suna Americanah, labari ne na wata mata ‘yar Najeriya da ta je karatun jami’a a Amurka da kuma dawowarta Legas.

An samo labarin dake fim din Americanah ne daga wani littafi wallafar Chimamanda Ngozie Adichie, wanda ya yi fice har ya samu babbar kyauta a 2013.

Tun bayan sanarwar da kamfanin shirya fina-finai na WarnerMedia ta fitar a makon jiya, ‘yan Najeriya ke ta nuna adawarsu a shafin twitter, cewa bai dace a zabi Nyong’o ‘yar kasar Kenya, wacce ta taba lashe kyautar jarumar fim na Oscar ba, ta fito a matsayin ‘yar Najeriya a fim din.

A cewarsu, zai fi dacewa a sanya ‘yar Najeriya da za ta iya magana da harshen ‘yan Najeriya ta fito a matsayin ‘yar kasar.

“Fitowar Lupita a matsayin zai fuskanci matsala daya… magana da harshen Ibo,” a cewar wani a twitter.

Wannan kuma na cewa: “Akwai kyawawan jarumai mata ‘yan Najeriya da za su fi iya yin abun da ake bukata.”

A nasu bangaren, ‘yan Kenya a shafin twitter sun yi ta kare zabin da aka yi wa Nyong’o, inda suke wa ‘yan Najeriya shagube da cewa ai ba Nyong’o ce ta “kawo rashin aikin yi a Najeriya ba” saboda ta zama kwararriyar jaruma.

Wasu kuma sun tunatar da ‘yan Najeriyar cewa ba a sanya dan yankin gabashin Afirka ko daya ba a wakar Beyoncé da aka sanya fim din ‘The Lion King’ wanda kamfanin Disney ya sabunta, duk da cewa an yi amfani da yanayin kurmin kasar Kenya wajen tsara fim din.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Duniya ta fara shaida illar harin da aka kai wa Saudiyya | BBC Hausa

Published

on

An ga hayaki ya turnuke bayan harin da aka kai kan wurin hakar mai na Armco da ke garin Abqaiq
Hakkin mallakar hoto
Reuters

Farashin mai ya yi tashin da bai taba yin irin sa ba cikin wata 4, bayan wasu hare-hare 2 da aka kai wa wurin hakar man kasar Saudiyya, wanda hakan ya sa aka samu nakasu na kashi 5 cikin dari na albarkatun mai da ake samarwa a duniya.

Gangar danyen mai ta Brent ta tashi da kashi 19 cikin 100 inda ta kai Dala 71.95 kan kowace ganga.

Duk da dai an samu sauki kadan bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da umurnin fito da mai daga rumbunan kasar ta Amurka.

Zai dai iya daukan wasu makonni masu zuwa kafin matatar man ta Saudiyya da abin ya shafa ta dawo aiki yadda ta saba.

Kamfanin tace mai na kasar Saudi Aramco ya ce harin ya sanya man da kasar ke samarwa ya yi kasa da ganga miliyan 5.7 a kowace rana.

Harin wanda aka kai da jirgi maras matuki ya hada har da wanda ya fada kan matatar mai mafi girma a duniya da ke kasar ta Saudiyya.

Amurka dai ta zargi Iran da hannu a harin.

Saudiyya dai ta ce tana kokarin kashe wutar, to amma da alama kokarin nata bai isa ba – Inji Abishek Kumar, wani jami’i a Interfax Energy.

Ya kara da cewa da alama barnar da aka yi wa cibiyoyin sarrafa man fetur din na Abqaiq da Khurais na da muni.

Iran ta zargi Amurka da kokarin yaudara, bayan da sakataren wan=jen Amurka din Mike Pompeo ya ce Iran ce ke da alhakin kai harin.

Mr Pompeo dai ya yi watsi da ikirarin da ‘yan tawayen Houthi na Yemen suka yi cewa su ne ke da alhakin kai harin.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Yawan hutawa na cutar da lafiya – amma yana da amfani ta wani bangaren BBC news

Published

on

Getty Images

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Duk wani ma’aikaci mai jajircewa da ya yi ritaya na fargabar yadda ranakunsa za su cika da rashin aikin yi.

Ga mutanen da suke ganin zuwa aiki shi ne gishirin rayuwarsu, suna ganin rayuwa ba za ta yi armashi ba idan ba sa zuwa aiki.

Duk da cewa zuwa aiki na cike ranakun mutum, ana iya ganin lokacin da za a bata nan gaba ba tare da ana wani aiki ba a matsayin mai cike da rudani kuma yana iya jefa mutum cikin wasu munanan ayyuka kamar shan kwayoyi.

“Daga bayanan da muka samu – da kuma la’akari da al’amura na yau da kullum – cewa mutane da yawa na fadi tashi a aiki,” in ji Andrew Yang, dan takarar shugabancin Amurka a jam’iyyar Demokrat kuma wanda ya kafa kungiyar samar da aiki ta Venture for America.

“Ba ma yin komai; ba ma aikin sa-kai sosai, duk da cewa muna da lokaci sosai. Sannan lokaci na tafiya sai mu fara buga wasannin komfuta da shan barasa. Al’umma gaba daya ba ta ci gaba idan babu aikin yi,” a cewarsa.

Yin hidima ya bambanta da aiki

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An san mutanen Japan da tsawon rai, suna yawan cikin kazar-kazar a kullum.

Aikin da ake biyan albashi ba shi kadai ne hanyar da ke kai ga rayuwa mai dadi ba.

Misali, ‘yan Japan suna da wata al’ada ta ikigai. Al’ada ce ta kara masu karfin guiwar samun farin ciki ta hanyar mayar da hankali ga wani abin da suke yi da zai sa su tashi da sanyin safiya.

Cikin ‘yan kasar Japan da aka gudanar da bincike a kansu a 2010, binciken ya nuna cewa kashi daya bisa uku suna amfani da al’adar ikigai, sauran kashi biyu bisa ukun da suka rage, rashin albashi da soyayya da kuma mayar da hankali kan wasu hidimomi ya sa suka yi ritaya daga aiki.

Ba kullum ake hutawa a lokacin hutu ba

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

A wannan zamani, mata suna aikatuwa kwarai da gaske amma irin wannan aikin ba a daukar shi da muhimmanci kamar irin aikin albashi.

Misali lura da yara da kuma yin ayyukan gida da sauran hidimomi na cin sa’o’i dayawa.

Rage yawan aiki a ofis zai iya bayar da daman samun lokaci da kuma kuzari domin aiwatar da sauran ayyukan gida da hidimomi – amma kamfanoni da gwamnatoci kada su rage zuba jari a wasu bangarori saboda sun dogara da wasu su yi aiki kyauta.

Hutun karshen mako mai tsawo

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Za ku iya aikin sa-kai?

Wani bincike da aka gudanar kan gajeren hutun karshen mako ya nuna ma’aikata masu dogon hutun karshen mako- amma wadanda albashinsu ba a kara masu ba – suna amfani da sauran lokutansu wajen yin abubuwa kamar buga wasan kwallon golf da sauran wasanni.

Alexandra Hartnall, wata mai aikin tuntuba kan kasuwanci da sadarwa a London ta ce ta gano cewa yin aiki a biya ta ya sa ta samu natsuwa, wannan ne ya sa ba ta yin aiki ya wuce na sa’o’i hudu a rana.

Hakan ba zai sa wasu su taimaki jama’a ba

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wani kalubale a nan shi ne ko da mutum ya samu saukin aiki kuma yana da lokaci ba shi zai sa lallai mutum ya yi wasu abubuwan da suka hada da taimakon al’umma ba.

Melanie Oppenheimer daga jami’ar Tokyo ta bayyana cewa a Australia wadanda ke tsakanin shekaru 35 zuwa 44, su ne suka fi yin ayyuka na sa-kai.

Dalili kuwa shi ne aikin sa-kai na da fadi ba kamar yadda mutane ke tunani ba: akwai buga wasan game na talabijin da kuma taimaka wa ‘yan ci-rani samun matsuguni da taimaka wa wasu masu aikin karatun kimiyya duk na cikin aikin sa kai.

A ra’ayin Oppenheimer, lokaci ba zai kasance kalubale ga irin lamarin ba, amma yana da kyau a taimaka wa masu son aikin sa-kai a kuma taimaka masu da dama idan ta samu.

Facebook Comments
Continue Reading
Advertisement
Advertisement

Trending

%d bloggers like this: