
Mutanen da basu gaza 6 ne ba ciki har da wata mata aka kashe a wasu hare-hare da aka kai kan wasu al’ummomi a kananan hukumomin Bassa da Mangu ta jihar Plateau.
Majiyoyi sun bayyana cewa mutane 12 da suka jikkata na can na samun kulawar likitoci a asibiti.
Mazauna yankin sun bayyana cewa hari na farko an kai shi ne a wajejen garin Ancha dake karamar hukumar Bassa a yayin da hari na biyu aka kai shi garin Gyenbwas dake gundumar Langai a karamar hukumar Mangu.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa harin na baya-bayannan ya faru ne kwana guda bayan da aka kashe wasu mutane hudu tare da jikkata wasu biyu da suka hada manoma da kuma Fulani makiyaya da aka kashe a garin Uwok-Ishe dake gundumar Kakkek a karamar hukumar Bassa akan hanyarsu ta zuwa wani wurin hakar ma’adanai.
Garba Abdullah, shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Gan Allah Fulani Development Association (GAFDAN) wanda ya tabbatar da faruwar hari na farko ya ce an ayyana bacewar mutanen ne da misalin karfe 3 na dare lokacin da suke kiwo inda aka kuma gano gawarsu a Ancha.
“Makiyayan suna tsaka da kiwo lokacin da maharan suka ja su daga inda suke kiwo ya zuwa Ancha suka kashe su.Mun kai rahoton faruwar lamarin wurin yan sanda da kuma rundunar Operation Safe Haven,” ya ce.
A Gyenbwas Rinji mutane biyu aka kashe ciki har da mace tare da kone gidaje da dama.